Gist
[Cutar Corona] Abinda ya sa aka dakatar da gwaji a Kano

Bayanai suna kara fitowa daga Kano dalilan da suka sa aka dakatar da gwajin cutar korona a Kano.
Bayanin farko da BBC ta samu shi ne an dakatar da gwajin ne saboda rashin kayan aiki na yin gwajin gano masu dauke da cutar.
Farfesa Sadiq Isah na kwamitin yaki da cutar korona a Kano ne ya tabbatar wa da BBC hakan a ranar Laraba, inda ya ce dole ce ta sa aka yi hakan don ba su da sinadaran da ake bukata don ci gaba da gwajin.
Sai dai daga baya, Farfesa Sadiq ya shaida wa BBC cewa an kai sinadaren gwaje-gwajen, amma ba za a ci gaba da aiki a dakin gwajin ba har sai bayan sa’o’i 48, kasancewar an yi feshin kashe kwayoyin cuta a dakin.
- A yi gwaji don gano ko coronavirus ce ke hallaka mutane a Kano – Farfesa Usman Yusuf
- Coronavirus: Tsawon wane lokaci ake dauka kafin a warke?
Farfesan ya ce a yanzu haka za a dinga kai gwaje-gwajen wadanda ake tunanin sun kamu da cutar Abuja, sannan a jira sakamakon su fito kafin a san karin wadanda suka kamu.
Daya daga masu gudanar da gwajin ya shidawa BBC cewa dama, ka’ida ce ana irin wannan feshin maganin a dakunan da ake gwaje-gwajen korona, kuma ba a ci gaba da aiki sai bayan wani lokaci.
Cibiyar ta Kano, wacce ke asibitin Malam Aminu Kano, na yin gwaji ga jihohi da dama na arewacin Najeriya.
Masana harkar lafiya dai na cewa gwaji na daya daga manyan hanyoyin yaki da cutar ta korona.
- Alamun Coronavirus: Abubuwan da suka kamata ku dinga yi
- Coronavirus: Yadda za ku kare kanku, da hana yaduwarta da bin shawarwarin WHO
Hukumar NCDC dai ta ce tana fadada cibiyoyin gwajin cutar ta korona a duka fadin kasar.
Akwai karancin cibiyoyin gwajin dai a arewacin Najeriya, inda mafi yawan cibiyoyin suke a kudanci.
Bayanai sun ce akwai fiye da cibiyoyi 20 a jihar Lagos na gwajin cutar, sai dai ba duka ne suka karkashin gwamnati tarayya ba.
-
FREE BEAT2 weeks ago
[Freebeat] Professional Beatz – Are You Playing Beat
-
Music2 weeks ago
Dj Tapezy Ft. Kizz Daniel X Tekno – Buga (Amapiano Retouch)
-
Mixtape2 weeks ago
Dj LaMszXy Ft. Mishasha – High Riddim Mad Mixtape
-
FREE BEAT1 week ago
[Freebeat] Dj Ozzytee X Dj Swagman – Soft Cruise Beat
-
Music2 weeks ago
Camidoh – Sugarcane Ku3h Amapiano Ft. Mayorkun X King Promise X Darko X Dj Kush